Tashin Hankali Tsakanin Matasan Somaliyawa a Canada Ya Hallaka Wasu da Dama

Abdulahi Hasan Sharif dan shekara 30 daga Somalia immigrant, ya shiga hannun 'yan sanda akan zargin kokarin kisan kai tare da kai hari da wuka

Al’ummar Somaliya da ke kasar Canada, ta ce fatara da rashin ayyukan yi da rashin sukunin makaranta na daga cikin dalilan fadawar matasanta cikin muggan kungiyoyi, wanda hakan ke kawo matukar cibaya ga matasan na ta.

Somaliyawa matasa fiye da dozin biyu sun halaka a Alberta saboda tashe-tashen hankula cikin shekara 10 da ta gabata, ta yadda aika-aikar ‘yan bangarsu ta yadu har zuwa Toronto ma, a cewar jami’ai.

Al’ummar ta ‘yan Somaliya mazauna Canada ta tattauna kan matsalolin mace-mace masu nasaba da ayyukan ‘yan bangan ne kwanan nan, a wani taron fayyace rayuwa da Sashin Somaliyanci na Muryar Amurka ya shirya a Toronto.

A shekarar 1991, wasu ‘yan Somaliya da dama da ke guje ma yaki a wannan kasa ta gabashin Afirka sun samu mafaka a wata unguwa da ke arewa maso gabashin Toronto