Tashe-tashen Hankula Da Talauci Sune Ke Janyo Safarar Mutane - MDD

Burundi

Majalisar Dinkin Duniya MDD tayi gargadin cewa tashe tashen hankula da talauci suna janyo safarar mutane da bauta, lamari da yake samarwa kungiyoyin miyagu dake wannan aiki dala milyan 150 a shekara daya a fadin duniya.

Babban sakatare na MDD Antonio Gutierrez, ya gayawa kwamitin sulhu na majalisar jiya labarin lokacin zama na musamman kan wannan batu cewa yanzu kungiyoyin nan za'a same su ko ina a fadin duniya. Zsa'a iya samun wadanda wannan musiba ta rusta da su a aksashen duniya 106.

Ana kiyasin cewa mutane milyan 21 ne wannan lamari ya rutsa da su, wadanda ake tilastawa yin ayyukan daban daban, mata suna karuwancin dole, wasu kuma ana tilasta musu shiga kungiyoyi da suke daukar makamai. Wasu ana tilsta musu yanke ko fidda wata gaba ko halitta kamar koda, domin a sayarwa mabukata.

Tashe tashen hankula a kasashen Syria, da Afghanistan da Somalia, da ma a wasu wurare daban daban sune suke samar da miliyoyin mutane wadanda suke cikin mawuyacin hali wadanda masu safarar mutanje suke amfani da su.