An jibge jami'an tsaro masu tarin yawa a wurin taron a birnin Fatakwal haka kuma aka baza jami'an tsaron a duk wata hanya da ta nufi wurin taron bisa umurnin babban sifeton 'yansandan Najeriya Ibrahim Idris.
'Yansandan sun yi anfani da hukumcin da wata kotun Abuja ta yanke ne na dakatar da taron kodayake wata kotu kuma a Fatakwal ta amince da taron.
'Yan jam'iyyar da suka zo daga sassa daba daban na kasar sun yi adawa da matakin da jami'an tsaro suka dauka. Alhaji Attahiru Bafarawa, tsohon gwamnan jihar Sokoto kuma dan kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyyar yace suna bin doka kuma sun bi dokar da ta basu izinin bin tsarin jam'iyyarsu.
Barrister Abdullahi Jalo yana cikin wadanda zasu yi takara a taron. Yace yanzu ta tabbata cewa APC nada hannu a kwatsanniyar kuma shugaban kasa ba zai ce bai sani ba. Yace akwai lauje cikin nadi.
Kabiru Aliyu sakataren jam'iyyar na jihar Zamfara yace idan babban sifeton 'yansanda zai bi umurnin kotu to ta Fatakwal inda aka shirya taron ya kamata ya bi.
Mr. Nick Dazan mai magana da yawun hukumar zaben Najeriya yace basu yanke shawara akan hukumcin da zasu bi ba, walau na kotun Fatakwal ko na Abuja.
Barrister Sadau Garba ya yi tsokaci akan hukumcin kotunan biyu dake karo da juna. Yace idan magana na kotu bai kamata wata kotu ta saurari maganar ba domin kada a samu hukumci da zasu yi karo da juna.
Ga rahoton Lamido Abubakar Sokoto da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5