An yi taron matasan masu bin akidar 'yan gurguzu a Niamey jamhuriyar Nijer.
WASHINGTON, DC —
Burin tawagogin matsa 'yan jam'iyyar gurguzu da suka fito daga koina a Afirka shi ne su karfafa fahimta da ganewa da shirin yadda zasu gudanar da harkokin gwamnati idan sun samu kansu a shugabnacin siyasa.
Matasan fiye da ashirin sun fito daga sassa daban daban na Afirka. Taron na son ya tallafa masu da koya masu yadda zasu tabbatar da cigaban dimokradiya a Afirka. Taron na kwana uku zai kaddamar da kasidu da koyaswa kan alkiblar da 'yan darikar gurguzu suka sa gaba a duniya.
Malam Salisu Hamadin daga jihar Bauchin Najeriya na daya daga cikin wadanda suka halicci taron. Ya ce akidar gurguzu ita ce ta samu galaba kamar yadda ta samu a kasashen China da Poland da irin su Rasha kuma rayuwa a wadannan kasashen ba irin ta kasashen jari hujja ba ne. Ya ce shi ya sa matasa manyan gobe idan suka koyi akidar gurguzu ba zasu samu matsala ba idan Allah ya basu shugabanci. Zasu yi anfani da koyaswar akidar gurguzu ta yadda al'umma zata anfana.
To amma taron ya zo daidai lokacin da kasashen dake milki irin na gurguzu ke cikin rigingimu da matsaloli ire-iren masu nasaba da rikicin siyasa. Malam Adamu Manzo mataimakin kungiyar 'yan gurguzu a jamhuriyar Nijer kuma dan jam'iyyar PNDS ya ce akwai wasu kasashen shekara da shekaru ana musgunawa matasan 'yan gurguzu.
A kasashe kamar su Bokina Faso 'yan gurguzu na dandana kodarsu. Sai dai kamar yadda wakilin kungiyar daga Bokina Faso ya ce suna nan suna gwagwarmaya a kasarsu domin waye kawunan mutane game da su. Ya ce ta hanyar zaman lafiya da kwanciyar hankali zasu canza duniya.
Ga rahoton Abdullahi Maman Ahmadu.

Your browser doesn’t support HTML5