A cikin hirarsu da Sashen Hausa shugaban kungiyar hadakar matasa Musulmi Mamman Lawal Mai Doki ya bayyana cewa, an shirya taron ne ganin yadda ake kara fuskantar kalubalar zamantakewa, inda ake fuskantar rashin jituwa da tashe tashen hankali tsakanin Musulmi da Kirista. Yace wannan taron zai bada damar fahimtar juna kasancewa ya hada kan mutane daga kabilu da addinai dabam dabam, Yace taron ya nemi bin tsari da magabata suka kafa kasar a matsayin kasa daya dunkulalliya.
Mahalarta taron da dama da Sashen Hausa ya yi hira da su, sunce wannan taron yazo daidai lokaci da ya dace musamman ganin yadda ake kara zaman doya da manja tsakanin Musulmi da Kirista, yayinda ake fama da rikicin Fulani da Makiyaya da kuma rikicin Boko Haram, da na ‘yan bindigar Niger Delta duk da yake wancan ya dan lafa, sai dai a matsayin kasa baki daya ana fuskantar kalubalar tsaro, da rikice rikicen da ake dangantawa da harkar siyasar kasar.
Shugaban kula da harkokin Da’awa na shiryar Kudu maso Kudu da kuma kudu maso gabashin kasar Uztaz Mohammad yace a daidai lokacin da ake neman mafita tsakanin Kiristoci da Musulmin najeriya akwai bukatar taro irin haka da zai taimaka wajen dinke baraka
Taron da aka saba gudanarwa duk shekara, ya sami halartar mai martaba Sarkin Musulmi Mahammad Sa’ad Abubakar , da shugabannin addinin Kirista, da kuma wadansu shugabannin al’umma daga arewacin kasar, inda aka gabatar da jawabai da kasidu
Wadanda suka gabatar da kasidun da suka hada da Limaman Kirista da Musulmi da kuma sarakunan gargajiya sun maida hankali a jawabansu kan bukatar zaman lafiya inda aka jadada bukatar Kirista da Musulmi su rungumi juna.
Ga cikakken rahoton Lamido Abubakar.
Your browser doesn’t support HTML5