Taron Kyautata Hanyoyin Amfani Da Kafafen Sadarwar Zamani

A karon farko da aka kaddamar da taron karawa juna sani na kasa-da-kasa, akan muhimancin kafafen yanar gizo a shekarar 2010, duk masu halartar taron sun yima kafafen kallon wata sabuwar hanya da zata kawo sauki ga al’ummah, musamman wajen isar da sako da karfafa zumunta a fadin duniya.

Yanzu haka an fara taron karo na 10 a birnin Toronto dake kasar Canada, take taron na wannan shekarar shine “Bayanan sirri cikin aminci” taron zai maida hankali akan irin baccin rai da mutane suka fuskanta a sanadiyyar amfani da kafafen sadarwar zamani.

Farfesa Anatoliy Gruzd, na jami’ar Ryerson ya shaida hakan, inda yake cewa, mutanen na kara fahimtar alfanu da akasin amfani da kafofin sadarwar zamani. Wane irin cutarwar kafafen keyi ga masu amfani da su, wanda basu tsaya kawai ga mutum da kanshi kawaiba, har da sauran harkokin rayuwar yau da kullun.

Taron dai ya kara maida hankali akan ire-iren illoli da kafafen ke haifarwa, don ko a ‘yan kwanakin baya sai da shugaban Amurka Donald Trump ya gayyaci wasu kafafen sadarwar zamani fadar ta White House, inda ya ke cewa wasu kafafen suna nuna mishi wariya.

Daya daga cikin mahalarta taron Farfesa Valerie Steeves, ta jami’ar Ottawa tace ai yanzu matasa da ma dattawa suna taka tsan-tsan akan ire-iren abubuwan da suke rubutawa a shafukan nasu, ba kamar yadda su keyi abaya ba shekaru 10 da suka shude.