A taron na shekara-shekara da kungiyar Fulanin take gudanarwa a garin Jos, al’ummar fulanin da suka fito daga sassa daban-daban na Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Burki Na Faso da sauran kasashen Afirka, sun koyar da junansu muhimmancin nuna ‘kauna ga kowa da inganta zamantakewarsu da sauran al’umma.
Shugaban kungiyar Rev Buba Aliyu, yace dalilin taron shine su yi cudanya da ‘karfafa juna don yin sulhu da kowa. inda yace sun yiwa shugaban ‘kasa da gwamnatoci addu’o’i.
Mutanen da suka ziyarci wannan taro sun nuna gamsuwarsu da muhimmancin zaman lafiya a duniya. Ita dai kungiya Fulani mabiya addinin Krista ta kwashe shekaru 40 tana gudanar da al’amuranta.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5