A taron sun bada shawarwari akan yadda za'a shawo kan matsalolin.
Taron ya tattaro kananan kabilu daga jihohi goma sha biyar dake shiyar.Sanata Shen Zagbai Nuhu daga jihar Neja shi ne shugaban taron. Yace sun yi taron ne domin su ne ba'a damu dasu ba da irin wahalolin da suke fuskanta. Misali, rashin tsaro su ya fi shafa, su da matansu da 'ya'yansu. Yanzu da zabe ke karatowa yace ba zasu jefawa kowa kuri'a ba sai an yi masu alkawarin cika masu bukatunsu.
Suna bukatan a kula dasu kamar yadda ake kulawa da wasu. Idan an zo sa mutane gwamnati a tabbata an sa mata da maza daga bangarensu. Abu na biyu shi ne batun tsaro.
Tare da tsaro gwamnati ta gyara kasarsu ta kuma inganta rayuwarsu. 'Yan kudu sai su zo kasashensu su fisu kudi domin duk wasu hanyoyi da zasu bi an hanasu. Abubuwan da yakamata a yi masu ba'a yi ba. Na gabansu kuma sun yi gaba. Babu waiwaya baya domin a samu a tafi tare. Suna son matasa su natsu. Su bar shaye-shaye, su kaunaci juna su kuma gayawa junansu gaskiya.
Sun yi korafin an kone masu coci, an kashe masu mutane da jam'an tsaro da suka fito daga cikinsu kuma har yanzu babu abun da gwamnati tayi a kai. Abun da wasu jihohi suke samu a arewa su basa samu. A wannan zabe mai zuwa ba zasu amince da rikicin bayan zabe ba. Wai zasu dakile shi , su hana.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5