Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo Addo ya kalubalanci takwarorinsa dake kan jagorancin gwamnatocin Afirka, da su amince da yiwuwar fasahar hada-hadar kudi (finTech) wajen haifar da ci gaban tattalin arziki, ta hanyar yin aiki don kawar da shingayen da ke kawo cikas ga yin amfani da wannan fasahar (ta fintech).
Yace, Nahiyar Afirka na iya shawo kan kalubalen da take fuskanta ta hanyar zuba hannun jari a wannan fasahar domin yin gogayya da kasashen da suka ci gaba a duniya.
Shugaban Ghanan, ya jefa wannan kalubalen ga takwarorinsa ne, a wajen bude taron koli na kwanaki uku kan kirkire-kirkire, tasiri da zuba jari, ko 3i Africa Summit a birnin Accra.
Ghana na karbar bakuncin babban taron na 3i Africa Summit a turance, da ke da nufin bunkasa fasahar dijital da fasahar hada-hadar kudi tsakanin kasashen Afirka don ci gaban tattali arziki ta hanyar zuba hannun jari mai dorewa na dogon zango.
Taron wanda aka yi wa taken "Bunkasa fasahar hada-hadar kudi (FinTech) da Tattalin Arziki na Dijital a Afirka," Bankin Ghana (BoG), da Bankin Raya Ghana (DBG), da kuma Hukumar Kula da Lamuni ta Singapore (MAS) suka shirya ya samu halartar shugabannin hukumomin kasuwanci kimanin 4,000 daga kasashe kusan 80.
A jawabinsa na bude taron, shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya jaddada wajabcin yin amfani da fasahohin da a halin yanzu ke sake fasalin tattalin arzikin duniya tare da daidaita su da bukatun nahiyar.
Yace, nan da shekarar 2035, AFCFTA na da niyyar fitar da 'yan Afirka kimanin miliyan 30 daga kangin talauci, tare da kara samar da kudaden shiga na kusan mutane miliyan 68 a lokaci guda.
Shugaba Akufo-Addo ya kara da cewa, ‘amma, domin wadannan fa'idodin su tabbata, tilas ne mu yi amfani da ikon fasahar zamani na fintech da sabbin kirkire-kirkire na dijital.
Tilas ne mu rungumi fasahohin da ke sake fasalin tattalin arzikin duniya ta hanyar da za su yi mana aiki, tare da daidaita su da bukatunmu na musamman da kuma magance kalubale da nahiyarmu ke fuskanta.’
Shi kuma Sakatare-Janar na yankin cinikayya tsakanin kasashen nahiyar Afirka mara shinge ko (AfCFTA), Wamkele Mene, ya bayyana cewa, ‘Dalilin da ya sa aka kafa yankin cinikayya tsakanin kasashen nahiyar afirka mara shinge, domin mu yi amfani da wannan kasuwa mai yawan mutane biliyan 1.4, wanda a shekarar 2050 ake hasashen za ta kasance ta 8 mafi karfin tattalin arziki a duniya da dala tiriliyan 16.3; shekaru 27 daga yanzu.
Amma idan ba mu yi amfani da wadannan fasahohin na zamani ba, sai dai mu tattauna inda muka yi kuskure.’
Masani kuma mai sharhi kan tattalin arziki, Sarki Imurana Hashiru Dikeni yace wannan taron zai taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin Afirka, idan muka yi la’akari da cewa, abokan cinikayyar Afirka, musamman kasashen Yamma, sun fi samun amfanin kasuwancin da suke yi.
Domin haka, idan an tabbatar da fasahar hada-hadar kudi da wasu fasahohin kasuwanci zai taimakawa nahiyar domin, ‘A zamanin nan ba za a samu ci gaban ciniki ba sai da fasahar harkokin kudi. Aikin da ya kamata a yi cikin shekara sai a iya yin shi gaba daya cikin wata guda saboda muhimmancin fasahar.’
Duk ra'ayoyi da kuma mafita da aka dace a cikin kwanaki uku na taron kolin, za a tattara su a matsayin shawarwari, yarjejeniyoyin haɗin gwiwa, manufofin ci gaba da za su taimaka wajen kaddamar da fasahar fintech da tattalin arzikin Afirka mai dorewa, sai a mika su ga shugabanni a fannin kuɗi, da wadanda abin ya shafa don aiwatarwa.
A saurari cikakken rahoton Idris Abdullah:
Your browser doesn’t support HTML5