Mrs. Nosiviwe Nqakula, ministan tsaron Afirka ta Kudu, tace a wani lokaci cikin shekarar nan zamu yi taro na musammam tsakanin ma’aikatan kasashen biyu Najeriya da Afirka ta Kudu, inda za a yi musayar dabarun yaki da ta’addanci.
Ministan tsaron ta kara bayyana wasu sassa da suka hada da nuna dabarun kariyar sararin samaniya da Afirka ta Kudu zata gayyaci Najeriya, wanda za ayi a birnin Johannesburg a watan Satumba. Wannan dai hadin kan kasashen Afirka biyu masu tasiri na da muhimmanci a yunkurin kungiyar Afirka AU wajen yaki da ta’addanci.
Shima ministan tsaron Najeriya, Mansur Dan Ali, yace “muna duba yadda kasashen namu guda biyu zasu hadu da sauran manyna hafsoshin soja domin a fito da wata manufa da kasashen biyu zasu amfana…” inda ya ci gaba da bayyana yadda yaje kasar Afirka ta Kudu, ya gano kayayyakin aikin da Najeriya take bukata, har ma su taimakawa Najeriyar wajen kera makamai da ake a jihar Kaduna.
Domin karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5