Taron Fasahar Duniya Na Bana, Mai Taken Duniyar Yau A Dunkule

Kimanin dubban mutane ne ake sa ran zasu halarci taron bajekolin na’urorin zamani, da za’a gabatar a birnin Las Vegas dake kasar Amurka. Taken na bana shine “Duniyar Yau A Dunkule.”

Wasu daga cikin na’urori da za’a gabatar sun hada da na’urar Alexa ta kamfanin Amazon, mai amfani da murya wajen tantance mutane, da motoci masu sarrafa kansu da makamantansu.

Sababbi daga cikin na’urorin da za’a gabatar a wajen, zasu nuna irin cigaban da ake kara samu a duniyar fasaha, na’urorin dai na hada mutane da sauran abubuwan duniya a cewar Steve Koenig, mataimakin shugaban kungiyar masu amfani da na’urorin zamani ‘Consumer Technology Aossociation.’

An samu cigaba matuka cikin shekaru 30 zuwa yau, inda a da na’urorin kan hada mutun da mutun, amma a wannan karnin na 21 na’urorin na hada wata na’ura da wata.

Steve ya kara da cewar, a wannan shekarar mutane zasu cigaba da nuna damuwar su akan matsalar kutse, amma ba dai karancin cigaba ba a fannin fasahaba. Kadan daga cikin abubuwan da ke da ban sha’awa tare da na'urorin da za'a gabatar a bana shine, Sifika mai sarrafa kanta da kararrawar gida mai dauke da hoton bidiyo.