Taron farfado da tattalin arzikin Najeriya ya maida hankali ne akan noma

Shugaba Buhari a taron bitar farfado da tattalin arzikin Najeriya

A karshen babban taron bita akan makomar tattalin arzikin Najeriya na kwanaki biyu da aka yi a karkashn jagorancin shugaban kasa Muhammad Buhari da mataimakinsa an cimma matsayi a kafa kwamitin da zai sa ido kan aiwatar da duk manufofin da taron ya tsayar

Taron ya cimma yarjejeniyar inganta noma da hako ma'adanai domin farfado da tattalin arzikin kasar.

Kowane yankin na Najeriya, kai wace jiha ma dole ta noma wasu ababe guda biyu da zata dogara a kai su kuma wadatar da duk kasar. Kenan kowace jiha ta shahara ta kuma kware akan akalla abubuwa biyu da zasu wadata kasa da kuma sayar dasu a kasashen ketare da zummar samun kudin shiga.

Bayan taron gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru ya bayyana cewa ko sjhakka babu sha'anin noma shi ne makomar Najeriya domin za'a sayar da duk abun da aka noma a cikin gida da kasashen waje.

Yanzu kafin a cimma wannan burin sai an inganta noma yadda alabarkatun zasu habaka ba irin noman gargajiya ba na hannu kwarya hannu baka. Bisa irin adadin filin da ake samun tan biyu kawai na shinkafa a Najeriya a wasu kasashen adadin wannan filin kan bada shinkafa tan goma sha biyar ko fiye da haka. Dole ne sai kasar ta bi sabon tsari da hanyoyin zamani. Yanzu Najeriya na cin shinkafa wajen tan shida amma tan biyu kawai take nomawa. Dole a canza wannan lamarin.

Shi ma gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari yace komawa ga noma ya zama wajibi domin dogaro ga mai ba zai kai kasar koina ba.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron habaka tattalin arzikin Najeriya ya maida hankali ne akan noma - 3' 43"