An bayyana taron ECOWAS na wannan karon da cewa faduwa ce ta zo daidai da zama, ganin taron na aukuwa ne a daidai lokacin da Nahiyar Afirka ke ji da wasu kalubaloli masu tsanani. Dr. Usman Mohd Shugaban Cibiyar Horas Da ‘Yanmajalisa a Afirka, kuma malami a Jami’ar Jahar Kaduna ya fadi a hirarsu da Maryam Dauda cewa taron na da matukar muhimmanci. Ya kara da cewa taron zai tattauna kan batun tsaro da batun ta zarce da juyin mulkin da aka yi a Burkina Faso da kuma kokarin kwaskwari kundin tsarin mulki da wasu Shugabannin Afirka kan yi da dai sauransu.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ECOWAS ba ta daukar mataki sai barna ta faru, sai ya ce ga dukkan alamu al’amura za su kyautatu. Ya yi misali da yadda zabe ya ingantu a Ghana da kuma a Najeriya fiye da yadda abin yake a baya. Ya kara da cewa wadanda ake zaba – daga Shugaban kasa zuwa na kasa – duk za su dukufa wajen aikinsu saboda zabarsu cikin sahihanci da aka yi.
Da aka tambaye shi ko ya na ganin taron zai yi nasara a abin da ya sa gaba, sai ya ce idan aka yi la’akari da yadda aka samu shugabanci mai kyau a Najeriya fiye da yadda abun ya kasance a baya, za a yi nasara saboda hakan zai yi tasiri kan a bin da za a yi a taron.
Your browser doesn’t support HTML5