Taron Dalibai Ya Gamu Da Cikas

Kungiyar dalibai ta kasar Nijar, wato USN ta shirya babban taro da ya hada dukan kungiyoyin dalibai na kasar, inda za su sabunta kudurin kungiyar

Shi dai wannan taron na kungiyoyin daliban da aka shirya a jihar Agadez, suna yin shine domin sabunta kudurin kungiyar, sai dai a bana an samu wani hargitsi tsakanin daliban alhali taron ya maida hankali kan zaman lafiya tsaro da hadin kai.

Sumana Gambo Saini, magatakardan kungiyar ta USN ta kasar yace da ace duk ‘yan kungiyar sun je taron da lissafin nasara ko akasin haka tunda sha’ani ne na zabe tabbaci hakika da hakan bai faru ba.

Shi kuwa Changa Chalinbo, mamba, a kungiyar daliban jami’ar, Damagaram, ya nuna rashin dacewar hargitsin idan akayin la’akari da mauduin da aka sag aba watau zaman lafiya, hadin kai da tsaro.

Shi ma Gwamnan jihar Agadez, Sa’adu Soloke, ya yaba da mauduin da daliban suka maida hankali a kai, abinda yace ba karamin cigaban kasa bane.

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Dalibai Ya Gamu Da Cikas - 2'48"