A wani yunkurin tunatar da ‘yan Jarida tsarin aikin yada labarai a irin wannan lokaci da ake fama da annoba, kungiyar RENJED da hadin guiwar OXFAM DANEMARK sun shirya wani taron mahawara a cibiyar ‘yan Jarida dake birnin Yamai, inda aka tantauna akan wani matsakaicin kundi mai kunshe da muhimman ka’idodi da dokokin aikin yada labarai a Jamhuriyar Nijar.
Zaman zullumi da annobar cutar coronavirus ta haddasa wani yanayi a kasashen duniya da ke bukatar taka tsan-tsan a ayukan ‘yan Jarida don kaucewa yada bayanan da ka iya haifar da rudani a cikin al’umma, musamman a wannan lokaci na kafafen sada zumunta na zamani.
Wannan ya sa kungiyar RENJED da takwararta ta kasa-da-kasa wato OXFAM suka tsara wani matsakaicin kundi domin tunatar da manema labarai wasu mahimman ka’idodin wannan aiki.
Shugaban RENJED Ousman Dambaji ya ce, ya kamata ‘yan Jarida sun rika aiki bisa kwarewa kuma kamar yadda dokar kasa tsara, haka zalika Kuma su kiyaye yada labaran da za su iya kawo rudani a cikin al’umma.
An yaye wannan kundi a wani taron da ya hada jami’an hukumar tace labarai da masanan doka daga ma’aikatar shari’a da ‘yan jarida.
Dokokin aikin watsa labarai a Jamhuriyar Nijar sun tanadi wasu matakai da ke baiwa ‘yan kasa ‘yancin samun bayanai daga jami’an kasar a hukumance, to sai dai da alama ‘yan jarida na wasa da wannan dama.
Bayan Yamai, masu ruwa da tsaki a wannan aiki na fadakarwa da tunatarwa za su zagaya jihohin Maradi, Zinder da Tahoua domin gabatar da wannan kundi ga ‘yan jarida a matsayin wani makamin aiki.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Your browser doesn’t support HTML5