Taro Kan Cutar AIDS Ya Shiga Wuni Na Biyu

Taron kasa da kasa kan cutar kanjamau a birnin Washington DC.

Taron kasa da kasa kan cutar kanjamau da ahalin yanzu yake gudana anan birnin Washington DC, zai fi maida hankali ne kan bincike, matakai da ake dauka da hada kai wajen yaki da cutar.

Taron kasa da kasa kan cutar kanjamau da ahalin yanzu yake gudana anan birnin Washington DC, zai fi maida hankali ne kan bincike, matakai da ake dauka da hada kai wajen yaki da cutar.

Taron da ake yi bayan ko wani shekaru biyu litinin din nan zai shiga wuni na biyu, ana sa ran sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton zata yi jawabi a zaman taron nay au.

Jiya lahadi aka bude taron tareda yin kira ga gwamnatoci su ci gaba da samar da kudade domin yaki da wan nan cuta duk da matsalolin kasafin kudi da suke fuskanta.

Majalisar Dinkin Duniya tace akwai mutane milyan 34 wadanda suke fama da wan nan cuta. Mutane milyan daya da dubu dari bakwai ne cutar ta kashe a 2011.

Ana sa ran mutane fiyeda dubu ashirin ne zasu halarci taron wanda aka yi wa taken “Sai Mun hada karfi da zamu sami nasara kan kanjamau”.