A yayin hidimomin zagayowar ranar kare muhalli ta duniya, jiya Talata MDD ta bayyana tarkacen robobi a zaman daya daga cikin abubuwa masu matukar hadari ga muhalli a duniya.
A rahoto mai taken, "Robobin Amfani A Yar: Hanyar Daidaita Al'amarin," MDD ta ce a yayin da aka samu cigaba sanadiyyar ka'idojin da gwamnatoci kan kafa na amfani da tarkacen roba ta wajen barnar, wannan bai wadatar ba, kuma akwai bukatar gaggauta daukar karin matakai.
"Duniyarmu na mamaye da tarkacen robobi masu hadari," a cewar Sakatare-Janar na MDD Antonio Gutterres a wani jawabinsa. "Burbushin tarkacen robobin da ke cikin teku sun fi taurarin da ke sararin Subahana yawa."
"Tun daga tsibiran da ke can lungu zuwa yankin Artic, babu inda abin bai shafa ba. Muddun hakan ya cigaba, zuwa 2050 sai tarkashen robobi sun fi kifi yawa a cikin teku" a cewarsa.
Rahoton ya kuma lura cewa bisa kiyasi, kayan robobi kimanin tiriliyan 5 ake amfani da su a duniya a kowace shekara.