Tarayyar Turai ta gargadi Najeriya ta farfado da fitar da albarkatun gona

Ana wanke waken soya

A wani taron karawa juna ilimi wani jami'in tarayyar turai ya gargadi Najeriya ta farfado da fitar da albarkatun gona zuwa kasashen waje.

Wani jami'in kungiyar tarayyar turai dake ziyarar Najeriya ya bayyana bukatar Najeriya ta sake dawowa da matsayinta na fitar da wasu anfanin gona kamar yadda ta keyi kafin ta samu man fetur.

Wadan nan albarkatun gona kuwa sun hada da kwarin manja zuwa auduga da kuma gyada abun da yace zai karawa kasar kudin shiga.

Wakilin tarayyar turan yana jawabi ne a birnin Legas wurin taron inganta harkokin tsaftace kayan abinci da ake fitarwa zuwa kasashen turai.

Idan za'a iya tunawa kwanakin baya ne kungiyar tarayyar turan ta dakatar da shirinta na sayen wake da ridi da dai sauransu bisa zargin cewa ana sanya magungunan kashe kwari wanda ya wuce misali abun da kuma yake da illa ga bil Adama.

Alhaji Kabiru Bawa Rijau na kamfanin Afri Food ya halarci taron ya kuma yi bayani akan abun da kamfaninsa ke yi na inganta abinci tare da fitar dashi kasashen waje. Yace su suna bin ka'ida. Basa kuma sa magungunan da aka haramta ko sa wadanda aka amince dasu fiye da kima.

Akan hanyoyin da manoma zasu bi su kaucewa karya ka'ida Alhaji Kabiru Bawa ya yi bayani. Ya kira manoma su dinga kula da yadda suke sa magungunan kashe kwari

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Tarayyar Turai ta gargadi Najeriya ta farfado da fitar da albarkatun gona - 3' 49"