Taraba: Yajin Aikin Ma'aikatan Ma'aikatar Shari'a Ya Jawo Cikas a Harkokin Shari'a

Sanata Aisha Alhassan mai jiran kujerar gwamnan Taraba

Yanzu an kwashe watanni uku ma'aikatan ma'aikatar shari'a a jihar Taraba suna yajin aiki a fafutukar da suke yi na ganin an baiwa fannin shari'ar jihar damar cin gashin kansu kamar yadda wasu jihohi suka yi.

Yanjin aikin ya jawo cikas a harkokin shari'a saboda kotunan jihar sun koma tamkar kufai..

Yajin aikin ya jefa lauyoyi cikin wani rudani haka ma 'yansanda da ofisoshinsu inda suke fama da cunkoson masu laifuka da suka cika masu wuri. Ga kuma jinkiri wajen yanke shari'a.

Barrister Bilyaminu Lukman Maihanci wani dan rajun kawo sauyi a jihar ya bayyana halin da ake ciki a yanzu. Yace yajin aikin ya shafi aikinsu kai tsaye ya kuma shafi 'yancin al'umma. A ofishin 'yansanda akwai wadanda ake son a fitar amma babu halin yin hakan sai an je kotu. Ko ma'aikatan gidajen yari suna korafi akan yawan jama'a da yakamata an gama da su idan da kotuna na aiki. Ko 'yansanda jama'a sun yi masu yawa.

Gwamnati ta yiwa ma'aikatan alkawari amma har yanzu bata cika alkawarin ba amma kullum tana kiransu da su koma aiki.

Ita ma rundunar 'yansandan jihar ta koka da yajin aikin da ma'aikatan keyi. DSP Joseph Kwaji kakakin rundunar yace yanzu haka ofisoshinsu sun cika makil. Wadanda suka aikata laifuka da kuma aka gama bincike kansu suna nan har yanzu domin babu kotun da za'a kaisu.

Kwamred Muhammad Usman Karim shugaban ma'aikatan kotunan na jihar yace tura ce ta kaisu bango shi ya sa suka shiga yajin aikin domin tunawa gwamnatin yarjejeniyar da suka yi tun farko. Gwamnati ta nemi a bata wata uku ta aiwatar da bukatunsu amma bayan wa'adin ba'a yi komi.

Saidai gwamnan ta bakin hadiminsa na harkokin siyasa Alhaji Abubakar Bawa yace yajin aikin ba laifinsu ba ne. Yace tun kafin gwamnatinsu ta zo suke yajin aiki. Sun zauna dasu suka tattauna akan wasu abubuwa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba: Yajin Aikin Ma'aikatan Ma'aikatar Shari'a Ya Jawo Cikas a Harkokin Shari'a - 4' 03"