Yayin wannan taro,mai alfarma Sarkin Musulmi Alh.Sa’ad Abubakar, ya gargadi al’ummar kudancin jihar Taraba da su kai zuciya nesa don maido da kwanciyar hankali a yankin da yayi fama da tashe tashen hankula.
Da suke jawabi a lokacin bukukuwan Mr Shekarau Angyu, na biyu a matsayin babban basaraken kabilar Jukun, a Najeriya, Mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar, da kuma tsohon ministan tsaron Najeriya T.Y Danjuma, sun bukaci al’ummar kudancin Tarabanne da su kai zuciya nesa tare da kaucewa duk wani abu da ka iya kawo tashin hankali.
Tun farko a jawabinsa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ministan harkokin wasanni da matasa Barrister Solomon Dalung, ya wakilice shi ya ce dole sarakunan gargajiya su tallafa a yaki da cin hanci da rashawa da gwamnatinsa ke yi a yanzu.
“A kowace al’umma data cigaba akwai rawar da sarakuna iyayen al’umma ke takawa wajen kare al’adu da yaki da munanan halaye, ciki har da muguwar al’adar nan ta cin hanci da rashawa.
To sai dai kuma yayin da ake shagulgulan cika shekaru 40 na Aku Ukan, al’ummar yankin na Wukari, na ganin akwai wani hanzari da ba gudu ba game da halin da suke ciki a yanzu. Kawo yanzu dai hankula sun fara kwantawa a wannan yanki na kudancin jihar Taraba, wanda a baya ke neman komawa kufai sakamakon tashe tashen hankula dake da nasaba da rikicin kabilanci dana addini.
Ga rahoton Ibrahim Abdul’azizi daga Jalingo
Your browser doesn’t support HTML5