Don ganin yadda aikin ke tafiya, babban hafsan sojin saman Najeriyan ya kai ziyarar gani da ido zuwa tsaunin Mambilla don ganin yadda lamurra ke tafiya.
Darururwan mutane ne dai suka yi asarar rayukarsu ta sanadiyar tashe tashen hankula a kudancin jihar Taraba, ciki har da yankin na Mambilla dake da albarkatun kasa da ma'adinai.
To sai dai kuma yanzu haka tuni shirye shirye suka kan kama na samar da sansanin sojin sama da filin saukar jiragen yaki a tsaunin Mambillan don tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Da yake jawabi yayin wata ziyarar aiki da ya kai zuwa tsaunin Mambillan, babban hafsan sojin saman na Najeriya Air Marshal Sadiq Abubakar, ya ce akwai alamun nasara da nufin kawo karshen barazanar da harkar tsaro ke fuskanta.
Da yake mai da jawabi basaraken yankin ya ce su a shirye suke su bada hadin kai.
An dai dauki lokaci ana kallon tashi da lafawar rikicin da kan tada hankulan jama'a a yankin Mambillan.
Haka nan game da sauran matsalolin tsaro musamman Boko Haram, hafsan sojin ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu a yanzu.
Tarayyar Najeriyar dai na shirin fuskantar zabe a nan gaba kuma matsalar rashin tsaron na iya illa ga makomar zaben da ma watakila makomar kasar baki daya, kuma abun jira a gani dai na zaman nasarar ayyukan jami'an tsaron a kokarin sake dasa wata damba ta zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma a kasar.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5