Cibiyar kawo fahimtar juna tsakanin al'umma da ake kira Peace Initiative da kuma kungiyoyi masu zaman kansu suka yunkura domin wayar da kawunan al'umma.
Bishop Yohanna shugaban cibiyar yace abun takaici ne ganin yadda wasu 'yan siyasar jihar ke raba kawunan al'ummar jihar domin cimma bukatunsu. Yace tun shekaru aru-aru suke zaman tare a jihar mai kabilu daban daban da addinai daban daban. Yace a jihar kowane gida akwai Musulmi akwai Kirista. Basu saba da fadan addini ba.
Amma yanzu ana siyasa da gaba da kwace. Wasu sun dauka dole sai sun yi shugabanci. Yace amma Allah ne ke bada mulki da iko.
Shi ma Shaikh Mukhtar Abubakar Bali sakataren IZALA reshen jihar Taraba ya alakanta lamarin da rashin samun shugaba nagari. Dole a samu shugaba mai hangen nesa wanda ba zai kawo batun kabilanci ko addini ba. Ya kira shugabannin siyasa su zama shugabannin kwarai domin su samu hadin kan jama'arsu.
Yankin Wukari ya yi fama da tashe=tashen hankula. Mr. Benjamin Bako shugaban hadakar kungiyar Jukun ta Najerya ya bayyana dalilan rikice-rikicen. Ya bada hanyoyin magancesu .Yace a daina nuna banbancin addini ko yare. Yace don kana kirista ka samu shugabanci sai ka kwashe mukamai ka ba kiristoci da kabilarka. Irin wannan halin ne yake tsorata mutane.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5