Taraba: Rikicin Makiyaya Da Manoman Kabilar Kuteb

TARABA: Harin da makiyaya ke kaiwa a kauyukan Taraba

Yanzu haka an sake tura ‘karin jami’an tsaro zuwa yankin Takum da Ussa na jihar Taraba, biyo bayan kazancewar rikicin Fulani makiyaya da kuma yan kabilar Kuteb manoma.

Tun a safiyar Litinin har zuwa dare ake ta ci gaba da dauki ba dadi a wasu yankunan Takum da Ussan a tsakanin Fulani makiyaya da kuma yan kabilar Kuteb manoma, kuma kamar yadda rahotanni ke cewa an samu asarar rayuka da dama baya ga kauyukan da aka kona.

Mallam Tanko ‘Dan Azumi Kurmina, na cikin shugabannin Kuteb a jihar shine ya bayyanawa wakilin Muryar Amurka abubuwan dake faruwa a yankin, inda ma ya bukaci da akai musu dauki.

To sai dai kuma, shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Jauro Sahabi Mahmud Tukur, ya ce suma an kashe musu jama’arsu baya ga dabbobi.

Yanzu haka tuni aka tura ‘karin jami’an tsaro, inda sufeto janar na ‘yan sandan kasar ya tura wani jirgi mai saukar angulu tare da tura wasu manyan jami’an ‘yan sandan domin shawo kan lamarin.

ASP David Misal, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Taraba, ya bayyana halin da ake ciki da kuma matakan da aka dauka, koda yake ya musanta batun cewa fiye da mutum 20 aka kashe.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Taraba: Rikicin Makiyaya Da Manoman Kabilar Kuteb - 3'21"