Yayin da ya rage yan kwanaki kafin babban zabe a Najeriya, yanzu haka wata sabuwa ta kunno, inda a jihar Taraba jam'iyun hamayya ke zargin gwamnatin PDP da nuna barazana ga ma'aikata da kuma sarakunan jihar da ke dasawa da yan hamayya.
A wajen taron manema labarai a Jalingo fadar jihar, jam'iyun adawa sunce yanzu haka sun bankado wani shiri da suka ce gwamnatin jihar ke yi ta bayan fage kan ma'aikata da sarakuna game da zaben dake tafe.
Shima da yake nasa jawabin, daya daga cikin shugabanin kungiyoyin kwadago a Najeriya, wanda ke zama darakatan kamfen na daya daga cikin yan takarar gwamna a jihar, Kwamared Bobboi Bala Kaigama, ya nuna bacin ransa game da abubuwan dake faruwa yanzu, inda ya zargi gwamnatin jihar da shakulatin bangaro, ya ce lokaci yayi na kawo sauyi.
To sai dai kuma gwamnatin PDP a jihar ta musanta wadannan zarge zargen da yan jam'iyun adawa ke yi yanzu.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5