Kafin a samu a kammala filin saukan jiragen sama a Jalingo matafiya Abuja ko Kano ko Legas ta jirgin sama na daukan sa'o'i uku zuwa hudu kafin su kai filin saukar jiragen sama mafi kusa da Jalingo, wato Yola a jihar Adamawa.
Yanzu filin saukan jirgin saman Jalingo ya fara aiki. Wani jirgi ya dauko fasinjoji 48 a gwajin farko daga Abuja zuwa Jalingo. Cikin fasinjojin wani yace da sai sun dauki mota daga Jalingo zuwa Yola, sun yi tafiyar awa uku ko hudu saboda munin hanyar amma yau gashi sun taso daga Abuja kai tsaye zuwa Jalingo.
Samun filin yana aiki zai taimakawa ayyukan kasuwanci. Kasuwanci zai habaka domin maimakon mutane su bata lokaci zuwa Yola yanzu sai su tashi kai tsaye.Rashin hanyoyin mota masu kyau na jawowa harkokin kasuwanci da yawon bude ido cikas a jihar.
Gwamnan jihar yace ya baiwa gina filin fifiko ne domin sauwakawa maniyatta musulmai da kristoci masu zuwa aikin ibada. Haka kuma samun filin zai habaka ayyukan yawon bude ido zuwa wurare kamar su Mambila da Gashaka ko Kashinmila da sauransu.
Zuwa gaba ana iya fitar da albarkatun gona da jirgin sama daga jihar da kuma shigo da kaya zuwa cikin jihar.
Mazauna kauyukan dake kan hanya zuwa Jalingo daga Yola sun roki gwamnatin tarayya da ta sanya gina hanyar cikin kasafin kudi na shekarar 2016.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5