Tanzania Na Kimtsa wa Coronavirus

Wata kasuwa a kasar Tanzania

Ana fargabar cewa Tanzania na cike da hadarin samun bullar cutar saboda kwakkwarar huldar kasuwancin da take yi da China, inda tuni hukumomin suka sa ma’aikatan lafiyar kasar cikin shirin ko-ta-kwana.

"Mun dauki karin ma’aikata a tashoshin shiga kasar, sannan muna horar da su kan yadda za su iya gano cutar," a cewar Ministan lafiyar kasar Janeth Mgamba.

Ya zuwa yanzu Ministar ta ce suna da na’urorin gwajin zafin jiki 140 wadanda aka dasa su a filayen tashin jiragen kasar.

Baya ga haka, kwararru a fannin lafiya sun dukufa wajen fadakar da al’umar ta Tanzania kan yadda za su kare kansu daga cutar, inda ake kwadaitar da jama’a da su rike yawan wanke hannayensu da sabulu.

Sannan ana ba da shawarar cewa, idan mutum zai yi tari ko atishawa ya kare bakinsa da kyalle ko wani makari.