Fiye da 'yan kasar Burundi 500 ne aka maida da su kasarsu daga sansanonin 'yan gudun hijira guda uku da ke Tanzaniya a jiya Alhamis, matakin da ya zama na farko a gagarumin yunkurin da ake yi don mayar da mutanen da ke tserewa tashin hankali da rikice-rikice a shekarun baya zuwa kasashensu.
An saka kasar 'Yan Burundi a motocin bas-bas a sansanin Nduta, Mutendeli da Nyarugusu da ke yammacin Tanzania, inda za a dangana da su har zuwa wasu cibiyoyin karbar baki biyu a Lardin Ruyigi da ke kasarsu.
Bayan kuma sun kwana, za a tura su zuwa gidajensu a Lardunansu.
Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, sansanonin na Tanzaniya suna dauke da 'yan kasar Burundi kusan 184,000 wadanda za a tura su gida nan da karshen shekara nan, bisa yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla.
Suna kuma daga cikin ‘yan kasar Burundi kusan 350,000 da suka tsere wa rikicin siyasa a Gabas ta Tsakiya, wanda ya barke bayan wani zaben mai cike da takaddama da aka yi a shekarar 2015.