Tankar Mai Ta Kashe Mutum 57 a Tanzania

Wasu tankokin man fetur

A kasashe masu tasowa, jama'a kan dunguma wajen diban mai a duk lokacin da motar dakon mai ta fadi.

‘Yan sanda a Tanzania, sun ce akalla mutum 57 sun mutu, bayan da wata tankar mai ta fashe a garin da ake kira Morogoro a gabashin kasar.

A cewar ‘yan sandan, mutanen sun kone ne kurmus, sannan wasu da dama sun samu raunuka.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce mutanen sun gamu da ajalinsu ne, a lokacin da suka je kwasar ganimar mai, bayan da tankar ta tintsire, sanadiyyar hatsarin da ta yi a yau Asabar.

Shi dai garin Morogoro, ya kai nisan tafiyar kilomita 200 da Dar es Salaam, babban birnin kasar ta Tanzania.

A kasashe masu tasowa, jama'a kan dunguma wajen diban mai a duk lokacin da motar dakon mai ta fadi.