Gwamnan jahar Sakkwato kuma dan takarar gwamnan jahar a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya kira taron manema labarai jiya a fadar gwamnatin jahar, inda ya ce a yayin da hukumar zaben kan alakanta ayyana rashin kammalar zabe da tanajin dokar zabe, gwamna Tambuwal ya ce sun dubi kundin tsarin mulki da kuma tanajin dokar zabe ba su wannan tanaji ba. Ya kara da cewa hukumar zaben ba ta bayyana masu runhunan zaben da aka soke zabukansu da kuma dalilan da su ka sa aka soke ba.
Gwamna Tambuwal ya amsa cewa akwai dalilan da kan sa a soke zabe ta yadda ma na za a sake yi ba; akwai kuma dalilan da kan sa a soke amma kuma a sake wani sabo. Ya ce to amma hukumar INEC ba ta alakanta daya daga cikin irin wadannan yanayoyi da ayyana zaben jahar Sokoto a matsayin mara kammala da ta yi ba.
Gwamna Tambuwal ya ce ta na yiwuwa su ruga kotu su kalubalanci ayyana zaben a matsayin mara kammala. Ya kuma yi nuni da cewa akasarin jahohin da aka ayyana zabensu a matsayin marasa kammala ‘yan takarar PDP ne ke kan gaba. Sannan ya yi hanunka mai sanda ga jami’an hukumar INEC da cewa idon duniya na kansu.
Ga wakilinmu a Sakkwato Murtala Faruk Sanyinna da cikakken rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5