TAMBAYAR MU TA YAU A KAN : Auren Mace Fiye Da Guda Ga Masu Karamin Karfi

Sanusi Lamido Sanusi

Yayin da ake ci gaba da cece kuce akan tsokacin da mai martaba sarkin Kano Alhaji Sanusi Lamido Sanusi 2, yayi akan masu karamin karfi da auren mace fiye da guda, jama'a da dama na ganin yin hakan zai taimakawa al'umma ta hanyoyi daban daban, wasu kuma na ganin lamarin ba haka yake ba, mai zaku ce dangane da wannan lamari?

Ana iya ziyartar shafinmu na WhatsApp mai lambar waya +12025775834, "Dandalin VOA Hausa Group" ta yadda zaku rika aiko mana da sakonnin muryoyinku cikin sauki.

Ana iya aiko mana da sakon amsar wannan tambaya, ko kuma duk ra'ayoyinku kan abinda suka shafi matasa ta email zuwa ga Dandalinvoa@voanews.com