Taliban Ta Lashi Takobin Dauko Fansa

Majalisar dokokin Afghanistan ma ta yi Allah wadarai tare da bayyana takaicin yadda ba a sanya idanu kan sojojin kasashen waje a Afghanistan

Kungiyar Taliban ta lashi takobin dauko fansa a kan wadanda ta kira “Amurkawa marasa imani” a bayan da wani sojan Amurka ya kashe fararen hula 16, akasarinsu yara kanana, a yankin kudancin Afghanistan.

Jami’an Amurka da na Afghanistan sun ce wannan soja na Amurka mai mukamin saje ya fita daga cikin sansaninsu ya shiga gidaje a kauyukan dake kusa da nan a gundumar Panjwai dake lardin Kandahar, yayi ta harbe fararen hula yana kashe su jiya lahadi da asuba. Mutanen kauyukan suka ce ya cunna wuta a jikin wasu daga cikin gawarwakin mutanen da ya kashe.

Kwana daya bayan wannan, sojojin Amurka sun karfafa matakan tsaro a yayin da ofishin jakadancin Amurka ya gargadi ‘yan kasar dake Afghanistan game da yiwuwar hare-haren ramuwar gayya. Kungiyar Taliban ta fada yau litinin cewa zata dauko fansar ko wane dan Afghanistan da aka kashe.

Majalisar dokokin Afghanistan ta yi Allah wadarai da kashe-kashen fararen hular, ta kuma bukaci gwamnatin Amurka da ta hukumta masu laifi, ta yi shari’arsu a bainar jama’a. A yau litinin, ‘yan majalisar dokokin Afghanistan sun ce sun gaji da rashin sanya idanu a kan sojojin kasashen waje dake Afghanistan.

Wadannan kashe-kashe su ne na baya-bayan nan a jerin matakan da sojojin kasashen waje suka dauka wadanda suka harzuka ‘yan kasar ta Afghanistan. A watan da ya shige, an kashe mutane kusan 40 a mummunar zanga-zangar da ta biyo bayan kona al-Qur’ani da aka yi a wani sansanin sojojin saman Amurka.

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya nemi bayani game da wannan harin inda sojan na Amurka ya kashe yara kanana 9 da mata uku. Yace wannan kisan kai ne da aka yi da gangan a kan fararen hular da ba su ji ba ba su kuma gani ba, wanda kuma ba za a iya yafewa ba.

Shugaba Barack Obama na Amurka ya kira shugaban na Afghanistan jiya lahadi domin mika ta’aziyyarsa ga al’ummar Afghanistan. Har ila yau ya bayarda sanarwa yana fadin cewa wannan mummunan abu na alhini, kishiya ce ga kyakkyawan halin da aka san sojojin Amurka da shi da kuma irin yadda Amurka take mutunta al’ummar Afghanistan.

Jami’an NATO sun ce sojan, wanda mai mukamin saje ne daga wata runduna dake jihar Washington, ya mika kansa a bayan harbe-harben da yayin da asuba a Kandahar. Shaidu da dama sun ce ba mutum daya ne ya kai harin ba, amma jami’an Amurka sun ce sojan shi yayi wannan danyen aiki shi kadansa ya kuma mika kansa.

Jami’an sojan Amurka sun ce wannan soja yana da mata da ‘ya’ya. Suka ce sau uku ana tura shi Iraqi, amma wannan shi ne karon farko da aka tura shi kasar Afghanistan.