Talauci Da Kuncin Rayuwa Na Sa Matasa Shiga Boko Haram da 'ISIS.'

  • Ibrahim Garba

Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Kamar yadda tun da ake kyautata zato, wani bincike ya gano cewa talauci da kuncin rayuwa na sa matasa shiga kungiyoyi masu tsauraran ra'ayoyi

Talauci da kuncin rayuwa da kuma amfani da ikon gwamnati ba bisa ka'ida ba na ingiza matasa a Afirka zuwa cikin kungiyoyi masu tsauraran ra'ayoyi irin su Boko Haram da al-Shabab da kuma ISIS, bisa ga wani binciken Shirin Wanzar da cigaba na MDD, wanda shi ne irinsa na farko.

Binciken mai shafuka 124, wanda aka gudanar cikin tsawon shekaru biyu, ya ta'allaka ne kan tambayoyin da aka yi ma wasu mutane 495 masu samar da sabbin mambobi ma kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi.

Binciken ya bi diddigin dalilan da su ka sa matasa a Afirka ke sha'awar shiga kungiyoyi masu aikata ta'addanci, ya kuma bayyana yadda ake samun sabbin mambobin, da jahilcin da ke ciki, da kuma hadarin da ke dada karuwa, sannan rahoton binciken ya bayar da shawarwari kan yadda za a kawo karshen al'amarin.

"Rahoton ya gano cewa talauci ne ya yi shinfida ma hanyar shiga kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi," a cewar babban jagoran rubuta wannan rahoton kuma shugaban Shirin wanzar da cigaba ma MDD (UNDP) shiyyar Afirka, Mohammed Yahaya. Ya kara da cewa "Talauci, da danniya da rashin cigaba na taka rawa sosai a wannan al'amari a Afirka kuma saboda haka, ya kamata ma'abuta cigaba su shigo cikin fafatukar ta neman mafita."