Babbar kwamishinan kare hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatocin duniya da su mutunta hakkokin jama’a a daidai wannan lokaci na annobar COVID-19.
Michelle Bachelet ta fada a wata sanarwa yau Litinin cewa, bai kamata a take hakkokin bil’adama ba, da sunana matakan kariya na gaggawa akan annobar coronavirus.
Michelle, ta kara da cewa “Duk matakan da za’a dauka su zama na kariya, kada ya wuce ko ya yi kasa da hakan” kuma Kada mahukunta su yi amfani da damar wajen muzgunawa wadanda ba ra’ayin su daya ba, ko daidaita yawan jama’a, ko kuma tsawaita wa’adinsu akan mulki.
Ofishin babbar kwamishinar ya fitar da wasu sabbin ka’idoji na matakan gaggawa, wanda a cewar ta “Akwai rahotannin da dama da ke nuna cewar wasu ‘yan sanda da wasu jamai’an tsaro na amfani da karfi harma da makamai don tilastawa jama’a bin dokokin takaita zirga-zirga.”