Mahaifinsa Emmanuel Adama Mahama shi ne dan majalisa na farko da ya wakilci mazabar yammacin Gonja. Shi ne kuma Kwamishanan farko na Lardin Arewacin Ghana lokacin jamhuriya ta farko.
Bayan da ya kammala iliminsa a kasashen waje Shugaba Mahama ya koma kasarsa Ghana inda ya kama aiki. Daga shekarar 1991 zuwa 1996 ya yi aiki a matsayin jami’in labarai da al’adu da bincike a ofishin jakadancin Japan a Accra babban Birnin kasar.
Mutum mai mugun kishin kare marasa galihu, an fara zabar Shugaba Mahama zuwa majalisar dokokin Ghana a shekarar 1996 inda ya wakilci mazabar Bole da Bamboi har na tsawon shekaru hudu.
A watan Afirilun shekarar 1997 aka nadashi mataimakin Ministan Sadarwa. Bayan shekara daya likkafarsa tayi gaba yayinda ya zama cikakken Ministan Sadarwa a watan Nuwambar shekarar 1998.
Ya rike wannan mukamin na minista har zuwa watan Janairun shekarar 2001 lokacin da jam’iyyarsa National Democratic Congress (NDC) dake mulkin kasar ta danka ragamar mulki wa sabuwar jam’iyya ta New Patriotic Party (ko NPP) saboda kayen da ta sha.
A shekarar 2000 aka sake zabar Shugaba Mahama a matsayin dan Majalisar Dokoki mai wakiltar mazabar Bole da Bamboi na wani wa’adin shekaru hudu. An sake zabarsa akan wannan kujera a shekarar 2004 a karo na uku.
Tsakanin shekarar 2001 da shekarar 2004 Shugaba Mahama ya zama kakakin marasa rinjaye dake magana da yawun ‘yanmajalisar adawa. A shekarar 2002 ne kuma ya zama daraktan sadarwa na jam’iyyar NDC. A wannan shekarar ce ya shiga ayarin masu sa ido a zabukan majalisar dokokin Zimbabwe.
Yayinda yake rike da ma’aikatar sadarwa, shugaba Mahama ya zama shugaban hukumar sadarwa ta kasa wato N-C-A. A lokacin ne ya daidaita ayyukan sadarwan kasar har aka bar ‘yan kasuwa suka shigo ciki a shekarar 1997.
Shugaba Mahama ya cigaba da fadada muradunsa akan harkokin kasa da kasa. Ta sanadiyar hakan ya zama mamba na kawancen majalisun dokokin Afirka inda ya zama shugaban yankin Afirka ta Yamma. Bugu da kari a shekarar 2005 aka kara masa mukamin zama mai magana na marasa rinjaye akan harkokin kasashen waje.
Ranar bakwai ga watan Janairun shekarar 2009 Shugaba Mahama ya zama Mataimakin Shugaban Kasar Ghana.
Kamar yadda kundun tsarin mulki kasar Ghana ya tanada, Shugaba Mahama ya zama cikakken shugaban kasar Ghana ranar 24 ga watan Yuli na shekarar 2012 sanadiyar rasuwar shugaban kasar na lokacin, Farfasa John Atta Mills.
Shugaba Mahama yana auren Lordina Mahama kuma Allah Ya albarkacesu da ‘ya’ya bakwai. Shi dai mai bin addinin Kirista ne amma danginsa sun hada da Kiristoci da Musulmai. Yana da sha’awa akan harkokin yanayi musamman illar da leda ke yiwa Afirka wadda yayi kokarin shawo kanta lokacin da yake rike da mukamin mataimakin shugaban kasa.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5