Yau kasa da mako guda kenan da fara gasar cin kofin duniya a Rasha, amma tuni an zira kwallaye fiye da yadda wasu ke tsammani, wasu kwallaye da aka ci sun kasance na takaici, wasu na farin ciki, wasu ma na ban mamaki.
Amma a iya cewa wannan ba abin mamaki ba ne, idan aka yi la’akkari da cewa salon kwarewa a fagen ta maula a duniya a wannan zamani, ba abu ne da wata nahiya ko kasa ko club za ta ce ta fi kowa iyawa ba.
Shekaru da dama da suka gabata, akwai kasashen da idan za a yi kwallo da su, masu kallon sukan iya hasashen cewa su za su ci, saboda kwarewa da suka yi a fagen kwallon kafa.
Misali, idan muka dauki kasashe irinsu Brazil da Jamus, kasashe ne da kowa yake fargabar karawa da su a da.
Ko da yake, har yanzu ma ana fargabar haduwa da su, amma ba kamar da ba, domin kwallon yanzu aba ce mara tabbas – ina ga babu kuskure idan mutum ya ce kwallon kafa a yau aba ce da kamar kowa ya sha a ruwa.
Ba wai hakan na nufin dari bisa dari kowacce kasa ta iya kwallo ba ne a yau – da haka ne da Rasha ba ta lallasa Saudi Arabia 5-0.
Kamar yadda muka ambata a farkon wannan sharhi, a ‘yan kwanaki hudun nan da aka kwashe kasashe na kece raini, masoya kwallon kafa sun yi farin ciki, wasu sun sha takaici wasu kuma sun ga abin mamaki.
Duk da cewa batutuwa ne da suka riga suka faru, kuma da dama daga cikin masoya kwallon kafa a duniya sun gani, Sashen Hausa na Muryar Amurka zai yi bitar wasu daga cikin fitattun wadannan batutuwa da suka faru kamar haka:
Shin Saudiyya Ta Shiryawa Wannan Gasa? Ko da yake, kasar Saudiyya ba kasa ba ce da ta shahara a fagen wasan kwallon kafa, amma da yawa daga cikin masoya kwallon kafa ba su zaci Rasha mai masaukin baki za ta sha ta har kwallaye biyar ba, ba tare da ta rama ko da kwallo daya ne ba.
Najeriya Ta Shafawa Gemunta Ruwa Kuwa?
Mazauna yankin nahiyar Afirka da dama, sun yi ammanar cewa ‘yan wasan Najeriya za su iya fitar da nahiyar kunya a gasar, wato cikin kasashe biyar da ke wakiltar nahiyar a gasar. Wasu sun zaton Najeriya za ta shafawa gemunta ruwa bayan da Iran ta lallasa Morocco da ci 1-0, Uruguay ma ta doke Masar da ci 1-0. Amma sai ga shi Najeriyar ta sha mamaya a hannun Croatia da ci 2-0.
Messi Da Bugun Fanarti
Kwararren dan wasan Argentina, Lionel Messi (Barcelona) ya zubar da bugun daga-kai-sai-mai-tsaron-raga a wasansu da Iceland, kwallon da a ce ya ci, za su samu cikakkun makinsu uku. Idan ka kalli yadda ya yi da fuskarsa da yadda ya buga hannayensa cike da takaici bayan da ya zubar da fanartin, ba sai an fada maka ba, shi kansa ya san cewa ya dama kunun da ba zai shawu ba.
Uwa uba - gabanin faruwar hakan, Cristiano Ronaldo, (Portugal/Real Madrid) dan wasan da ake mai kallon abokin hamayyar Messi ne, ya ci kwallaye ‘yan-uku (hartrick) a wasansu da Spain. Hakan ya sa shafukan sada zumunta musamman Twitter ya rincabe da muhawarar da aka saba ta waye gwanin gwanaye a tsakanin ‘yan wasan biyu.
Hmmmmm! Waye Ya Hango Hakan?
Wankin hula ya kai mai rike da kofin gasar dare. Wa ya za ci Jamus za ta sha kashi a hannun Mexico, ko da yake dama, ai Mexico ba kanwa lasa ba ce a fagen wasan kwallon kafa, amma duk da haka tarihi ya nuna cewa rabon da Mexico ta samu nasara akan Jamus tun a shekarar 1986.
Ana Wata Ga Wata
Brazil ta bi jerin manyan kasashen da suka yi ta fadi tashin ganin sun lashe wasansu na farko, amma abin ya cutura. Tawagar 'yan wasan ta Brazil sun yi zargin cewa, 'yan wasan Switzerland sun yi ta wasan kura da Neymar, lamarin da ya hana shi sakat, zargin da Switzerland ta musanta.
Akalla katunan gargadi (yellow cards) har guda uku aka ba 'yan wasan Switzerland. An tashi a wasan 1-1.
Daga Nan Sai Ina?
Wadannan batutuwan da suka faru cikin kwanaki hudun da aka fara karawa a gasar ta cin kofin duniya, ba lallai ba ne a ce haka tafiyar za ta ci gaba.
Ta iya yiwuwa dukkanin kasashen da ba su tabuka komai ba su yunkuro su ba da mamaki – idan har sun dauki darasi daga abin da ya faru a baya.
Amma dai ‘yar manuniya ta nuna cewa, ba lallai ba ne mutum ya yanke matsayar cewa ga kasar da za ta lashe wannan kofi – komai na iya faruwa.
Yanzu kasashen Afirka biyu ne suka rage su gwada kaiminsu a wannan sabon mako da aka shiga.
Tunisia za ta kara da Ingila a yau Litinin, yayin da Senegal za ta kara da Poland a gobe Talata.