A kasar Guinea, a kalla mutum ‘daya ne ya rasa ransa, mutane da yawa suka ji rauni a Conakry babban birnin kasar, a lokacinda jami’an ‘yan sanda su ke kokarin dakile wata mummunar zanga zanga da ake akan gwamnatin shugaba Alpha Conde.
Jam’iyyun masu adawa ne suka bukaci, ayi wannan zanga zangar domin matsawa gwamnatin kasar lambar, ta yi zaben kananan hukumomi kafin ayi zaben shugaban kasa, kamar yadda yarjejeniyar da yan siyasa suka kullaa shekara ta 2013 ta tanada.
Gwamnatin kasar bata amince da ‘bangaren yarjejeniyar akan zaben ba, a saboda haka ta shirya yin zaben shugaban kasa a ranar sha ‘daya ga watan Agusta, sa’anan kuma ayi zaben kananan hukumomi a farkon shekara mai zuwa.
Gwamnatin dai tayi kira domin a tattauna cijewar da aka samu, amma shugabannin ‘yan adawa sun ki yarda da duk wani tattaunawa har sai an canza lokacin zaben.