Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Ahmed Lawan shi ne ya kara jaddada muhimancin fitowa fili a yi wa 'yan kasa bayanin yadda daukan matasan zai gudana domin a kaucewa yawan zargi da ake yi na yin almundahana a shirin.
Ahmed Lawan ya ce ba a taba Gwamnatin da ta yi irin wannan yunkuri na ba matasa aiki irin wannan Gwamnatin ba kuma Majalisar ita ce ta amince da kasafin kudi Naira biliyan 52 domin a gudanar da aikin tun farko.
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce lallai sai Majalisa ta gamsu da yadda shirin zai gudana kafin a dawo da shi.
Abin lura shi ne cewa tun da aka fara batun daukan aikin ne aka yi zargin cewa an ba 'yan majalisar, da Gwamnoni kaso 15 cikin 100 na guraben daukan aikin.
Sai dai Kwararre a fanin Kundin Tsarin Mulkin kasa Barrista Mainasara Ibrahim ya ce Majalisa ba ta da hurumin dakatar da wannan shiri duk da cewa su ne masu yin dokoki sannan kuma su ne masu sa idanu a yadda bangaren zanraswa ke gudanar da ayyukanta yana mai cewa a nan hurumin su ya tsaya.
Shi ma mai nazari a al'aumuran yau da kullum Alhassan Dantata Mahmood ya ce baiwa 'yan Majalisar guraben aiki abu ne da ake yi a matsayin na alfarma amma babu dokar da ta ba da damar a basu.
Wannan dai shi ne karo na farko da yake nuna fito na fito tsakanin majalisar ta 9 da bangaren shugaban kasa.
Saurara karin bayani a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5