Bankin Raya Kasashen Afirka ya ce har yanzu “bai cimma wata matsaya” ba kan bukatar da Amurka ta gabatar na a gudanar da wani bincike kan shugaban bankin.
Wani mai kwarmata bayanan sirri ne ya yi zargin ana take ka’idojin gudanar da harkokin bankin, a cewar kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP.
Sakataren Baitulmalin Amurka Steven Mnuchin ya ce hukumomin Washington ba su gamsu da wani binciken cikin gida da aka gudanar kan Cif Akinwumi Adesina ba, wanda ya wanke shi daga dukkan zarge-zargen da ake masa.
Shugabar kwamitin amintattun bankin na AfDB, Niale Kaba, wacce ita ce Ministar raya kasa a vory Coast, ta ce kwamitin da aka kafa don ya binciki lamarin, ya zauna a ranar Talata domin “duba korafe-korafen” da mai kwarmata bayanan ya yi akan Adesina.
Amma a cewarta “babu wata matsaya da aka cimma, kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar da harshen Faransanci.
Sanarwar har ila yau ta kwatanta zarge-zargen da ake yi akan shugaban bankin a matsayin “zuki ta malle,” da kafofin yada labarai suke yadawa.
A dai ranar Laraba wasu kafafen yada labarai suka ruwaito cewa kwamitin amintattun bankin ya yi na’am da bukatar da Mnuchin ya gabatar, wacce ta nemi “a kafa wani kw amitin bincike kwakkwara daga wajen bankin,” domin duba korafe-korafe da ake yi akan Adesina.
A dai farkon shekarar na ne, wani mai kwarmata bayanan sirrin ya yi zargin cewa matsalolin yin wadaka da kudaden bankin da nuna wariya sun yi wa bankin katutu karkashin shugabancin Mr. Adesina.
Adesina shi ne dan Najeriya na farko da ya fara shugabantar bankin na raya kasashen Afirka wanda aka kafa shekara 56 da suka gabata.