Kamfanonin man Shell da Malabu Oil and Gas da Muhammad Sani Abacha su ne suka zuba hannun jari a rijiyar mai din mai lamba 245.
Onarebul Razak Atunwa shi ne shugaban kwamitin binciken badakalar rijiyar Malabu. Yace sau biyu Majalisar Wakilai ta nemi shiga cikin batun domin a sasanta.
Yace an yi kokari a shekarar 2003 da kuma shekara 2014 amma an gagara gano bakin zaren.
Razak yace akwai badakalar cin hanci da zamba a batun wanda ya shafi wadansu manya. Rijiyar tana nan ba'a komi da ita sai rikici akan wadanda suka zuba hannun jari a cikinta..
Razak ya ce zasu yi kokarin warware rikicin saboda bincike ya nuna cewa rijiyar tana da danyan mai fiye da ganga biliyan tara kuma a dan karamin lokaci zata iya samarwa kasar kudin shiga har dalar Amurka biliyan shida kwatamkwacin Nera biliyan dari biyar.
Alhaji Lawal Abba wakilin Muhammed Sani Abacha yace waccan yarjejeniyar da suka yi da ta sabawa dokokin kasa da na duniya iko ne na shugaban kasa ya soke kana a yi wata sabuwa.
Idan an yi sabuwar yarjejeniyar sai a dawowa masu rijiyar na ainihi, wato gwamnatin tarayya da kamfanin Malabu.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5