Gwamnatin jihar Nasarawa tace takaddamar dake tsakaninta da ma’aikatan jihar kan albashi ya biyo bayan rage rarar kudin data dora akan albashin ma’aikatanne bayan tayi la’akari da cewa kudin shigarta a yanzu sun ragu.
Mataimakin gwamnan jihar Mr Silas Agara, ya bayyana cewa babban dalilin da yasa aka sami damuwa shine yanayin da tattalin arzikin kasar ya shiga, shiyasa suka duba yadda zasu daidaita lamarin albashi domin bayaga tsarin albashin da gwamnati ta kayyade, akwai kudaden rara ko bonus a turance da gwamnatin jihar take karawa ma’aikatanta. Ta dalilin haka ne suka janye wannan kari, amma a cewar sa, har yanzu suna biyan albashi kamar yadda gwamnati ta tsara.
A bangaren jama’ar da suka gudanar da zanga zangar goyon bayan matakin da gwamnatin jihar ta dauka kuma, sun bayyana cewa wannan kyakkyawan mataki ne da gwamnatin ta dauka domin kuwa hakan zai taimaka masu domin jama'a da dama na neman abinyi koda kuwa kudin da za'a biyasu bai kai yadda ake biyan ma'aikatan jihar a yanzu ba.
Shugaban majalisar shiga Tsakani na gamaiyar kungiyoyin ma’aikatan jihar ta Nasarawa malam Sule Odeh Usman, yace babbar matsalar data sa su shiga yajin aikin shine sabon tsarin biyan albashin da gwamnatin jihar ta shigo da shi.
A daya bangaren kuma, shugaban kungiyar kwadagon jihar comrade Abdullahi Adeka yace wannan batu ne da kungiyar tasu zata nemi maslaha tsakaninta da gwamnatin jihar.
Ga Zainab Babaji da cikakken rahoto.
Your browser doesn’t support HTML5