A taron manema labarai da ya kira kakakin hedkwatar sojojin Najeriya Birgediya Janar John Agim ya ce atisayin tseren bera da suka yi a wasu johohin dake tsakiyar Najeriya ta yi nasara amma sun yi asarar sojoji 13 tare da wasu bakwai da suka jikata.
A cewarsa shugabannin kungiyoyin fararen hula sun taka rawar gani wurin samun nasararsu sai dai ya zargi wasu hukumomi a jihar Taraba da kin hada kai da sojoji. Ya yi misali da karamar hukumar Takum da ta ki hada kai da bataliya ta 93. Maimakon hada kai dasu shugaban karamar hukumar ingiza jama’a ya yi akan sojoji, injishi.
Sai dai gwamnatin jihar Taraba ta bakin Mr. Anthony Danburam, kwamishanan yada labarai na jihar ya mayar da martini. A cewarsa shi bai san tushen zargin da sojojin suka yi ba. Yace sojoji kamata ya yi su hada kai da gwamna domin a kansa ne tsaron jihar ya rataya. Idan kuma bai samu hadin kan sojojin ba babu abun da zai fada. Ya ce azo ana kashe jama’arsa, idan yayi magana sai kuma a zargeshi.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5