Tun bayan da jam’iyyar PDP mai mulkin Najeriya ta yanke shawarar cewa shugaba Goodluck Jonathan ne dan takarar ta a zaben shugaban kasa na shekarar 2015, hakan ya janyo cece-kuce akan cancanta ko rashin cancantar sa a dokance ganin an rantsar da shi har sau biyu.
Barista Muhammad Tukur dake jihar Kaduna, yayi fashin baki akan batun a wata hira da suka yi da Ibrahim Ka-almasih Garba ma’aikacin sashen hausa na muryar Amurka, inda yace lallai kundin tsarin mulki ya ambaci batun cewa duk wanda yayi rantsuwa sau biyu bai kamata ya sake yi ba. Amma kundin bai yi Karin haske ko tanade-tanade ba akan yadda za a yi, wanda hakan ke kawo rigingimu Yanzu haka. Wasu sun nuna cewa akwai hukuncin kotun koli wanda yace bai kamata shugaban ya sake tsayawa ba, wasu kuma sun ce hukuncin bai shafi shugabanci ba.
Karin Bayani akan Rahoto na Musamman a Kan Boko Haram: Jini, Hawaye da Fargaba a Daular El-Kanemi >>
Barrister Muhammad ya kara da cewa, tabbas an rantsar da shugaba Jonathan sau biyu; bayan rasuwar tsohon shugaban kasa Alhaji Ummaru Musa ‘yar ‘aduwa da kuma lokacin da ya ci zaben shekarar 2011.
Baristan ya cigaba da cewa Bisaga inda kundin tsarin ya nuna bai kamata shugaba ya wuce wa’adin shekara takwas ba, wanda kuma idan haka ne, zarcewar shugaba Jonathan zata saba ma tsarin.
Daya daga cikin hujjojin da magoya bayan shugaba Jonathan suka bada itace, rantsuwar farko da shugaban yayi ta karasa wa’adin marigayi shugaba Ummaru Musa ne. Amma wasu kuma na ganin cewa bayan da ya maye gurbin Marigayin, ya sake ministoci da sauran wasu muhimman mukamai a gwamnatin kasar inji baristan.
Your browser doesn’t support HTML5