Tagwayen Asali wato Hassan da Hussaini 'Arewa Identical' - wani babban abun sha’awa ko al’ajabi da ya faru da wadannan tagwaye dai shine, baya ga cewar su tagwayen asali ne na gaske, hatta zanen yatsun su ''Finger Print' iri daya ba banbanci.
Wanda hakan abu ne mai yiwuwar faruwa kasancewar kowanne dan adam na da nasa shaidar yatsu daban da na dan uwansa.
Matasan sun bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sa aka sa masu suna tagwayen asali shine daga lokacin da suka je ofishin da ake yin Fasfo, na'ura ta kasa banbance zanen yatsun su.
Ku Duba Wannan Ma Mahaifiyar Jaruma Nafisa Abdullahi Ta RasuTagwayen asali dai mawaka ne amma na Afro-hip hop wanda suka ce suna tunanin bunkasa harshe da al’adar Hausa ta hanyar waka –sannan suna ingausa a wakar wato hada harshen Hausa da ta Turanci.
Sun ce wani babban abin da ke ci masu tuwo a kwarya kafin suyi fice shine suna fuskantar matsala musamman ganin cewar mawaki baya samun karbuwa da kansa idan zai fitar da waka sabuwa har sai ya alakanta kansa da wani fitaccen mawaki a maimakon shi kansa ya fara kuma ya samu karbuwa daga al'umma.
Babban burinsu dai shine su sami karbuwa kuma su yi suna kamar yadda mawakan kudancin Najeriya suka sami karbuwa a fadin kasar, zuwa saurann sassa a duniya.
Your browser doesn’t support HTML5