Tafiya Sannu Kwana Nesa Mata A Nemi Ilimi - Fatima Shehu

Fatima Shehu Yakasai

Fatima Shehu Yakasai – matashiya wadda ta sami fannin koyarwa lamarin da ya jefa ta cikin kuncin rayuwa domin ba abinda ta so ta karanta Kenan ba a makarantar gaba da sakandire, a cewarta ta so ta karanta harkar lissafi ko akawu, kasancewar kuriciya da kyar iyayeta suka shawo kanta har ta amince ta karanta fannin koyarwa.

Malama Fatima, ta ce ko da ta fara karatun sai ta ta fahimci cewar mafi amfani shien fahimtar abinda ake koya mata, dan haka sai sha’awar karatun ta shiga ranta, ta kuma kara da cewa bata fuskanci wani kalubale ba a yayin da take karatu sai dai matsalar rashin samun aiki da ta yi da wuri.

Ku Duba Wannan Ma Idon Kukai Karatu Zaku Samu Daukaka A Duniya: Wahida Isma'il

Ta ce bayan kammala karatun, ta sha gwagwarmaya kafin ta sami aikin yi amma a karshe ta sami koyarwa wanda da shi ne ta fara kuma a yanzu tana karatun ta na digiri na uku.

Daga karshe ta bukaci mata matasa su jajirce wajen neman ilimi , tare da cewar babban burinta a rayuwa shine ta ga ilimi ya inganta, kamar yadda ta bayyana irin rashin jin dadin ganin dalibai a makarantar gaba da sakandire amma basa gane harshen da ake koyar da su.

Your browser doesn’t support HTML5

Tafiya Sannu Kwana Nesa Mata A Nemi Ilimi - Fatima Shehu