Tabargazar Kasafin Kudi: Abdulmumini Jibrin Ya Ce Bai Gudu Ba

  • Ibrahim Garba

Hon Abdulmumini Jibrin

Yayin da ake ta cece-kuce kan inda aka kwana game da batun tabargazar kasafin kudin Najeriya da kuma inda tsohon Ciyaman din Kwamitin Kasafin Kudin Majalisar Wakilan Najeriya Honorabul Abdulmumini Jibrin, sai gashi ya tabbatar cewa zai dawo muddan aka bukaci ya bayar da ba'asi don sahihin bincike.

Tsohon Ciyaman din Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Alhaji Abdulmummuni Jibrin ya ce batun wai ya gudu zancen banza ne kawai. Ya ce wadanda hankalinsu ya tashi saboda karar da ya kai hukumar yaki da almundahana ne ke ta yada cewa ya gudu.

Abdulmummuni Jibrin, wanda a yanzu haka ya ke London, ya ce zai koma Najeriya duk lokacin da ake bukatarsa don bayar da ba’asi. Ya ce musabbabin zuwansa London shi ne karbar wata lambar yabo da wata kafar labarai ta bashi – to amma ba zai koma Najeriya ba har sai an dau mataki kan almundahanar da ya fallasa da kuma masu yin barazana ga ransa.

Alhaji Abdulmummuni Jibrin ya ce babu yadda zai tsaya a Najeriya ya na yaki da cin hanci da rashawa muddun ransa na cikin irin wannan hadarin ba tare da an dau mataki ba.

Ga cikakken hirarsa da abokin aikinmu Usman Kabara:

Your browser doesn’t support HTML5

Tabargazar Kasafin Kudi: Abdulmummuni Jibrin Ya Ce Bai Gudu Ba