Shugaban Amurka Donald Trump yace Ta’addanci da Koriya Ta Arewa sune manyan batutuwan dake ajandar taron kolin shuwagabannin kungiyar Kasashe bakwai masu arziki ta duniya, wanda aka fara shi a yau Juma’a a Sicily, tsibiri mafi girma a yankin tekun Bahar Rum.
Yayin da yake zaune a gefen Firai ministan Japan Shinzo Abe, Shugaban na Amurka yace zaman tattaunawar zai maida kai “musamman akan matsalar Koriya ta Arewa.”
Duk da cewar Ta’addanci zai kasance cikin muhimman batutuwan da shuwagabannin zasu takala a yayin tattaunawar kwanaki biyun da zasu yi a wannan tsibiri na kasar Italiya, shugaba Trump yace ci gaba da gwajin makaman nukiliya da masu linzamin da Koriya ta Arewa keyi, “babbar matsala ce da ta shafi duniya baki daya. Za a warware ta nan gaba, ina tabbatar muku za a warware,” in ji shugaban na Amurka.
Harkar cinikayya ita ma batu ne babba a wurin takwarorin aikin shugaba Trump da suka hallara a garin shakatawa na Taormina dake tsibirin.
Suna fatan sassauto da matsayin shugaban na Amurka game da cinikayya da kuma sauyin yanayi.