Ta Yaya Iyaye Zasu Hana Matasa Anfani Da Kafofin Sada Zumunta Ta Hanyoyin Da Basu Dace Ba A Lokacin Azumi?

Yayin da ake ci gaba da ibada cikin wannan wata na Ramadan, mamatasa samari da 'yan mata da dama na amfani da wasu kafofin sada zumunta na wayar hannu ta hanyoyin da basu dace ba, ta yaya iyaye zasu shawo kan irin wannan matsala?

Muna bukatar ra’ayoyin maza da mata akan wannan tambaya, kuma za’a iya aiko mana da sakon ta murya a kafar sada zumunta ta WhatsApp mai lamba +12025775834. Kada a manta a fadi suna da kuma jiha ko gari.

Ana iya sauraren wannan shiri a duk lokacin da ake bukata a shafinmu mai adireshi www.dandalinvoa.com