Ta Kashe Danta Saboda Talauci

Wata matashiya mai shekaru talatin da takwas (38) ta kashe jaririnta ba tare da wani tantama ba saboda kudi.

Ita dai wannan matar mai suna Kwaseve Fagal, wace ta fito daga kauyen Garkerko, dake karamar hukumar Keana, dake jihar Nasarawa, tace tsananini talauci ne ya damesu da ita da minjinta da kuma ‘ya’yansu. duk da cewa Manomi ne mijin nata.

Ta kara da cewa abin da zasu sa abakin salati ya gagara shi yasa da wani boka Alhaji Abass Loko, daga jihar Kaduna ya yimata tayin taimakamata da tsafi domin zaman mai kudi zai ta amince.

Ta bayyana haka ne alokacin da ake niunata ga manema labarai a hedkwatar ‘yan Sandan jihar, tana mai cewa a lokacin da Bokan yayi mata tayin tana da cikin wata shida ne (6) koda yake ta san cewa da dan dake cikinta za a yi amfani amma ta amince domin fita daga kangin talauci.