'Yar Najeriya Ta Jefar Da Jariri A Cikin Shara

Jami’an ‘yan Sandan kasar Austria, sun cafke wata matashiya, ‘yan Najeriya, mai shekaru ashirin da bakwai, da laifin jefar da jaririnta a cikin sharar wani makewayi a Vienna, babban birnin kasar Austria.

Hukumar, jami’an ‘yan Sandan kasar ta Austria, tace tana yiwa matashiyar tambayoyi bisa mutuwar jaririn.

Kakakin ‘yan Sandan Raimund Schwaigerlenhner, wanda ya tabbatar da labarin ya ce an kai jaririn asibiti amma daga bisani ya cika saboda tsawon lokacin da yayi a cikin shara babu iskar shaka.

Ita dai wannan matashiyar uwa, da take kan hanyarta na zuwa Washington jirgin su ya yada zango ne a kasar Austria, inda nakuda ya kamata an fahimci cewa tana subar jini a lokacin da suke jiran jirgi ne mai zuwa Washington.

Bayan da aka cafke ta an kaita asibiti, inda ake duba lafiyarta.