Shehun malamin na magana ne a taron shekara na gidauniyar raya ilimi da makarantu da kungiyar ta gabatar a Abuja.
Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya ce tun kafa kungiyar ta dauki matakan kafa makarantu da jan hankalin jama’a wajen muhimmancin neman ilimi don kawar da jahilci da kuma bunkasa zamantakewar alheri tsakanin jama’a.
Malamin ya ce al’umma ba za ta shiga halin ni ‘ya su ba matukar ta na bin dokokin Allah da kuma hakan ke yin nasara ta hanyar ilimin sanin Allah.
Da ya ke karfafa muhimmancin ayyukan kungiyar na raya ilimi, Sheikh Hamza Adamu Abdulhamid ya ce kungiyar ta na da makarantu a ko ina a fadin tarayyar Najeriya inda jama’a kawai na bukatar shiga ne don samun karatu.
Mai masaukin baki a taron shugaban majalisar malamai na Abuja Sheikh Ibrahim Duguri, ya ce aikin cibiyar ilimi ta kungiyar da ke Abuja na ci gaba da gudana har kusan an kammala aikin ta.
Babban bako a taron tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya ce ba abun da jama’a za su bayar ya zama ya yi kadan ta hanyar gudunmawa ko zuba jari ga raya ilimi.
A yanzu haka JIBWIS ta tura malamai birane da kauyuka har ma da wasu kasashe na Afurka ta yamma don gudanar da tafsirin watan ramadan.
Domin Karin bayani ga rahotan.
Your browser doesn’t support HTML5